Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Shekaru 14 Ta Baiyana Dalilin Kin Tona Sa'ar Kakan Ta Da Ya Yi Mata Fyade


Wata matashiya mai shekaru 14 da haihuwa ta bayyana dalilin da yasa taki tona asirin wani tsohon soja Shu’aibu Ahmed, mai shekaru 70 da haihuwa ya yi ta yi mata fyade har ya kaiga yi mata ciki.

A cewar matashiyar, Ahmed ya bata kudi Naira 100, a karo na farko da ya yi amfani da ita, ta kuma kara da cewa ta barshi ya ci gaba da kwana da ita ne saboda ya yi barazaran hallaka ta.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa matashiyar mai shekaru 14, da haihuwa ta baiyanawa mujallar Vanguard yadda mutumin ya yi ta kwana da ita ba dan son ran ta ba, lamarin ya faru ne a unguwar Nupawa da ake kira Ago Takpa, a birnin Ibadan.

Mahaifin yarinyar ya gane cewa diyarsa na da juna biyu ne bayan makwabtansa sun bayyana masa cewar diyar sa na dauke da ciki wata biyar.

Matashiyar ta bayyana cewa “a shekarar data gabata ne ‘yar uwarta ta aike ta taje gidan mutumin da ake zargin domin ta amso mata faifan CD,

Ta kara da cewa “dana je na iske shi zune a kofar gidansa inda ya fada min cewa Faifan CD, na cikin gida ajiye akan tebur, shiga ta keda wuya sai kawai ya shigo ya yi maza ya kulle kofa, ya kama ni ya cire min kayan da nake sanye da su, sa’annan ya kwana da ni”.

“Na yi kokari inyi kuwwa sai ya rufe min baki ya ce idan na daga murya zai kashe ni, bayan y gama ne naga wani abu fari a jiki na, a lokacinne ya fada mani cewa ya yi amfani da ni ya kuma gargade ni da kada in fadawa kowa, tun daga wannan lokacin ya ke ta kwana da ni, kuma duk loacin da ya gama sai ya yi barazar kashe ni idan na fada ma wani”.

Daga karshe ta bayyana cewa ranar farko da ya kwana da ita ya bata kudi Naira 100, wani lokaci har 200 ya ke bata koda shike ta bayyana cewa ba kudin shi take kwadayi ba, tsoron barazar kisan da ya ce zai yi mata ne yasa take barinsa yana kwana da ita.

Ta ce “na kasa fadawa kowa saboda bana so in mut, ban dade da kammala ajin farko na makarantar sakandire ba, kuma lokacin da ya fara anfani da ni ban fara al’ada ba”.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG