Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman Khan Ya Baiwa Marada Kunya


Tiger Zinda Hai
Tiger Zinda Hai

Fim din shahararren jarumin nan na Bollywood Salman Khan, wanda suka yi tare da Katrina Kaif, watau Tiger Zinda Hai na cin karensa babu babbaka tun ranar 22, da aka sako fim din.

Shi dai wannan fim din an nunashi a gidajen kallo da dama a kasar Indiya, kuma ya samarda fiye da dalar Amurka miliyan talatin da biyu $32, a makon farko.

Fim din bacin kamsar da masu kallo da yake yi yana kuma samarda makudan kudaden shiga ga Bollywood, kuma akwai allamun cewa fim din zai cigaba da samuarda wadannan kudade.na tsawon lokaci.

Tun farko an kiyasta cewa fim din zai samarda kimani dalar Amurka miliyan talatin da biyu (32) a makon farko kamar yadda wani masanin kasuwanci Girish Johar, ya wallafa a shafinsa na Twitter, amma daga dukkan alamu ya wucce inda ake nufi.

Fim din na Salman Khan da Katrina Kaif, ya kasance wanda jama’a suka dade suna dako wanda kuma cigaba ne na fim din Ek Tha Tiger, wanda aka nuna a shekarar 2012.

A yanzu haka dai fim din Tiger Zinda Hai, a riba yake domin har ya maida kudinsa abinda aka koiyasta an kashe a shirya fim din da kuma tallata fim din dalar Amurka ashirin da hudu $24 million.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG