Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Daukaka Alkalan Tamaula Na Najeriya


Alkalan Wasa
Alkalan Wasa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta daukaka alkalan wasa ashirin da tara (29) ‘yan Najeriya, da bajen hukumar ta FIFA.

Kakakin kungiyar alkalan wasa na Najeriya, Kelechi Mejuobi, yace ashirin da biyu (22) daga cikin mazane inda bakwai (7) suka kasance mata.

Ya kara da cewa alkalan wasa uku Abubakar Ago, Hadiza Musa da Ushie Michael, da suka yi ritaya a maye gurbinsu da Abubakar Abdullahi, Patience Madu da Olayinka Olajide.

Wannan daukakar da alkalan wasan suka sami na nufin cewa zasu iya yin alkalancin wasa a koina, a duniya, an dai gudanar da bikin ne a birnin Kano a tarayyar Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG