Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shafukan Sada Zumunci Na Taimakawa Wajen Gano Cin Zarafin Jinsi A Najeriya


Amadi Onyekachi took to Instagram to speak out against a policeman who allegedly sexually assaulted her. (Photo by Declan Cooley)
Amadi Onyekachi took to Instagram to speak out against a policeman who allegedly sexually assaulted her. (Photo by Declan Cooley)

Amadi Onyekachi tace wani dan sandan Najeriya yayi mata fyade a tsakiyar watan oktobar da ta gabata, tace daga farko tayi tunanin ba za a taba bi ma ta hakkinta ba domin babu yadda za’ayi ta kai karar dan sanda wajen 'yan uwansa.

Maimakon haka sai tayi amfani da shafin sada zumunci na Instagram domin bayyana abin da ke ranta, daga bisani ta kwanta tayi bacci, cikin tsananin bakin ciki da tashin hankali.

Yayin da take bacci, rubutun da tayi a shafin nata wanda ya bayyana cin zarafin da aka yi mata ya ja hankalin mutane da yawa a Najeriya har da dama suka yi sharhi akai kuma suka ci gaba da yadawa.

A bayanin da ta dora akan shafin ta, Onyekachi tace wani jami’in SARS ne yai mata umarnin ta fita daga motar tasin da take ciki inda yace ita ‘yar damfara ce kuma karuwa, kana daga baya kuma ya kirata dillaliyar miyagun kwayoyi don haka yana bukatar ya caje ta.

“ Wannan la'anannen ya saka hannunsa cikin rigar mamana” a rubutun da tayi a ranar 16 ga watan Oktoba. “a yayin da nake ihu da kokarin fita daga motar sai ya tsoratar da ni yace zai yi min dukan tsiya idan ya sake jin na yi ihu.”

Bayaninta ya jawo hankalin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da kuma jami’in hulda da jama’a na jihar Kwara, wato garin da abin ya faru inda suka nemi Onyekachi domin ta zo ta bada bayanin da zai taimaka wajen gano wanda ya aikata laifin abinda tace mai sauki ne domin yana dingishin da ba zai boyu ba. Anyi nasarar gano jami’in kuma ana gab da gurfanar da shi a gaban kotu.

Onyekachi tace da ba ta bayyana abinda ya faru ba a kan kafar sada zumunci ba da babu yadda za’ayi a kama shi, don haka ne ta ke kira ga sauran mata da su fallasa duk cin zarafin da suka fuskanta domin a hukunta wanda ya aikata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG