Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool Na Bukatar Karin Kudi Akan Coutinho


Philippe Coutinho
Philippe Coutinho

Liverpool ta bukaci Karin kudi daga Barcelona kafin ta sayar mata da Philippe Coutinho, sakamon kamfanin Nike tayi shishigi wajan buga riguna dauke da sunan dan wasan wanda yake nuna alamun cewar dan wasan ya koma Barcelona abinda har yanzu ba'a kammala ba. Barcelona na ganin cewar dan wasan na iya kaiwa har fam miliyan £160 kafin ya taho gareta.

Napoli tace a shirye take da tabar dan wasan bayanta na gefen hagun mai suna Faouzi Ghoulam, dan shekaru 23, da haihuwa wanda ya koma kungiyar Manchester United akan kudi fam miliyan £53. Tace zata maye gurbinsa da dan wasan Benfica Alejandro Grimaldo mai shekaru 22 a duniya akan kudi fam miliyan £26.6.

Everton zata biya fam miliyan £25 ko a karba ko a bari kan sayen dan wasan gaba na Besiktas mai suna Cenk Tosun, ita kuwa Besiktas tana neman Karin fam miliyan £2 kafin cinikin ya dai daita

Huddersfield Town na zawarcin dan wasan Baya na Monaco mai suna Terence Kongolo dan shekaru 23 a matsayin aro, Arsenal tace Har yanzu tana kan batunta na ganin ta dauko dan wasan baya na Chelsea David Luiz. Everton ta matsa kaymi wajan ganin ta sayo Steven N'zonzi daga kungiyar Sevilla na kasar Spain, Westham tana zawarcin dan wasan Arsenal Theo Walcott.

Kungiyar Arsenal ta ce kofa a bude yake da ta sayar dashi ga duk kulob din da take da bukata

Chelsea tana kokarim ganin ta shawo kan dan wasan baya na Juventus Giorgio Chiellini mai shekaru 33, da ya dawo kungiyar ta duk da kasancewar dan wasan na shirin sabunta kwangilarsa da kungiyar ta Juventus.

Swansea City tana zawarcin dan wasan gaba na Westham mai suna Diafra Sakho, ita kuma Westham tana bukatar dauko ‘yan wasa biyu daga kungiyar ta Swansea mai tsaron bayanta Alfie Mawson, 23 da kuma dan wasan tsakiyar ta Ki Sung-yeung, 28.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG