Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Kasuwar Hada-Hada Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallo


A Yau litinin 1/1/2018 aka bude hada hadar y'an wasan kwallon Kafa na duniya inda kungiyoyin kwallon Kafa daga ko ina a fadin duniya ke yunkurin ganin sun nemo ‘yan wasan da zasu saya da kuma sayarwa domin a cigaba da fafatawa a wasannin Lig na kasashensu a shekarar 2018.

Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid tana shirye shiryen biyan kudi Fam Miliyan £120 domin ganin ta dauko dan wasan tsakiya na Chelsea, Eden Hazard, a watan nan. Manchester United ta ce tana fatan Paul Pgoba, zai taimaka mata wajan sa baki don jawo hankalin dan wasan gaba na Juventus, Poulo Dybala, da ya dawo kungiyar da taka Leda.

Har ila yau Mourinho, ya ce yana bukatar dan wasan Inter Milan, Joao Mario, ya dawo kungiyar domin maye gurbin Machael Carrick, mai shekaru 36 da haihuwa. Everton, tana shirin tattaunawa da kungiyar Sevilla, kan batun sayen Steven N'zonzi.

Dan wasan tsakiya na Schalke O4, Leon Gorezka dan shekaru 22 zai koma kungiyar Bayern Munich a matsayin kyauta bayan kwantirakinsa zai kare a kungiyar ta O4. Arsenal, ta nuna shi'awarta ta ganin ta dauko dan wasan baya na Chelsea, David Luiz, in kuma Chelsea ba zata sayar da shi ga abokiyar hamayyarta ta Firimiya Lig ba da yuwar dan wasan ya koma kungiyar Juventus, ta kasar Itali.

Tottenham ta ce bata wata gaggawa wajan sabunta kwantirakinsa, dan wasan bayan ta Toby Alderweireld, duk da kasancewar kwantirakinsa zai kare a 2019, Southampton tana bukatar dan wasan gefe na kungiyar Arsenal, Theo Walcott dan shekaru 28 da ya koma kungiyar a matsayin aro a wannan wata na Jaaniru.

Pep Guardiola, y ace yana nan kan bukatar sa ta ganin ya dauko Alexsi Sanchez, daga kungiyar Arsenal, ganin cewar dan wasan gaban sa Gribrel Jesus, ya samu rauni a gwiwarsa inda ake ganin zai iya shafe sama da wata guda yana jinya. Dan wasan gefe na West Bromwich, James McClean ya nemi afuwa daga wajan ‘yan wasan kungiyar su sakamakon juya baya da yayi cikin ganuwar da kungiyar ta yi a wasansu da Arsenal.

Wanda hakan yayi sanadiyar kwallon da ta shiga raga inda aka tashi a wasan 1-1 Arsenal ta ce a shirye take da ta sayar da dan wasan ta Theo Walcott, ga kungiyar da duk take bukatar sa tsakanin Southampton Everton ko Westham.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG