Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Ci Gaba Da Habaka


Manchester City ta ce tana shirin sayar da dan wasan Bayanta John Stones, mai shekaru 23, da haihuwa a karshen kakar wasan bana.

Dan wasan gaba na Tottenham dan kasar Spain Fernando Llorente, dan shekaru 33, da haihuwa ya bayyana buktarsa ta barin kungiyar domin komawa tsohon kulob dinsa Athletico Bilbao dake kasar Spain.

Manchester City, yana kan gaba wajan zawarcin dan wasan tsakiya na Napoli Jorginho mai shekaru 25 da haihuwa, tuni dai ta fara tattaunawa da wakilin dan wasan kan batun. Shugaban kungiyar Arsenal Ivan ya ce yana tsammanin tsohon dan wasan kungiyar.

Mikel Arteta, wanda yanzu yake matsayin Mataimakin Pep Guardiola a Manchester City, ya fi dacewa da maye gurbin Arsene Wenger, a karshin kakar wasan bana.

Amma a nasa bangaren, tsohon dan wasan kungiya Arsenal, Ray Parlour, ya ce babu wanda ya dace da maye gurbin Wenger da ya wuce Kocin Newcastle Rafael Benitez.

Wani Marubucin Labarin wasanni a kasar faransa ya ce Arsene Wenger yana da burin kasancewa Kocin tawagar kasar Ingila wata rana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG