Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Tauraruwar Victor Moses Ta Fara Haskakawa


Kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea, ta bayyana sunan dan wasan Super Eagles na Najeriya Victor Moses a cikin jerin sunayen ‘yan wasanta da zata zaba a matsayin gwarzon shekara a kungiyar na 2017/18

A cikin jerin sunayen akwai N'Golo Kanté, Eden Hazard, Willian, Andreas Christensen, César Azpilicueta da kuma Marcos Alonso.

Victor Moses, ya buga wasanni 32 a kungiyar ta Chelsea a wasannin bana ya jefa kwallaye 3 ya kuma taimaka aka jefa 3.

Ba wani dan wasan Najeriya da ya taba samun wannan lambar yabon tun 1967 kimanin shekaru 60 baya, Mikel Obi ne kadai ya lashe lambar yabo ta matashin danwasa a kungiyar Chelsea 2007.

Sai kuma Dominic Solanke da Fikayo Tomori suka taba lashe Kyautar ‘yan wasa masu kwazo na makaratan koyan kwallon kafa ta Chelsea a shekarar 2015/2016.

Kungiyar Chelsea za ta bayyana sunan wanda ya lashe gwarzon shekara ta bana a kungiyar, a taronta na shekara shekara da za ta yi a ranar Alhamis 10 Mayu 2018.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG