Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Wasu 'Yan Wasa Za Su Ci Kasuwa Bana


Kocin Manchester United Jose Mourinho, ya ce kulob din ba zai kasance daya daga cikin manyan kulob da zasu shiga hada hadar sayayya ba a kasuwancin ‘yan wasa na bana ba, yace kungiyar za ta "zuba jari ne kawai don inganta 'yan wasan ta da suke dasu a yanzu.

Tsohon dan wasan kasar Brazil Rivaldo, ya ce ya zamo dole Neymar yabar kungiyar PSG in har yana so burinsa ya cika na kasancewa gwarzon dan wasan kwallon Kafa na duniya.

Shi kuwa Ronaldinho cewa ya yi dan wasan tsakiya na Manchester United, dan kasar faransa Paul Pgoba, na iya zamo wa gwarzon dan wasan kwallon Kafa na duniya, amma hakan bazata yuwu ba sai ya girmama Kocin sa José Mourinho.

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya aika da sakon jaje ga takwaransa dan wasan Arsenal Mohamed Elneny, wanda dukan su ‘yan kasar Masar ne bisa raunin da ya samu a wasan da kungiyar sa Arsenal ta doke Westham da ci 4-1 a wasan mako na 35, a Firimiya lig na kasar Ingila, inda aka fitar da shi sakamakon raunin da ya ji a idon sawunsa. A bangaren Kocin kungiyar Wenger, ya ce sai anyi X-ray kafin nan a iya sanin tabbacin abinda ke faruwa game da dan wasan.

Kungiyar Arsenal a yanzu tana da damar dauko tsohon mai horas da kungiyar Barcelona Luis Enrique domin ya maye gurbin Arsene Wenger

Kasancewar kungiyar Chelsea, ta maida hankalin tane kan masu horaswa na Juventus Allegri da Kocin Napoli, Maurizio Sarri, su maye mata gurbin kocinta Antonio Conte.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG