Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Kasuwanci Da Zawarcin 'Yan Wasan Kwallon Kafa


Kungiyar kwallon Kafa ta Paris Saint-Germain na tattaunawa da wakilin dan wasan tsakiya na Manchester united, Paul Pgoba dan gane da dawowarsa kungiyar.

Ta gefe guda kuwa ita Manchester united, tana bukatar fam miliyan £140 ga duk kungiyar da take bukatar sayen dan wasan Manchester united dai ta saye danwasan fam miliyan £89 daga kungiyar juventus

Manchester city tana bukatar ganin ta dauko danwasan gaba na Leicester city dan kasar Masar maisuna Riyad Mahrez inda ta ware fam miliyan £65 wajan sayen sa a kakar wasa mai zuwa.

Westham tana bukatar saye na dindindin kan mai tsaron raga na Manchester city Joe Hart, wanda yake zaman aro a kungiyar

Kocin kungiyar Arsenal Wenger ya ce yana da karfin guiwar cewar dan wasan tsakiya na kungiyar Jack Wilshere zai sabunta kwantirakinsa a kungiyar zuwa wani dogon lokaci.

shi kuwa a nasa bangaren Kocin kungiyar Everton, Sam Allardyce ya matsa kaimi wajan ganin cewar ya dauko dan wasan na Arsenal Jack Wilshere's a matsayin kyauta a karshen kakar wasan bana in har bai sabunta kwantirakinsa a kungiyar ba.

Manchester united, tana zawarcin dan wasan gaba na Kungiyar Watford mai suna Richarlison mai shekaru 20 da haihuwa wanda kungiyar Bayern Munich, da PSG ke sha'awar ganin sun saye shi zuwa kungiyarsu.

kungiyar Arsenal tana duba yuwar sayar da dan wasan bayanta dan kasar Jamus mai suna Shkodran Mustafi, mai shekaru 26, da kuma dan wasan tsakiyarta Granit Xhaka dan shekaru 25 da haihuwa inda take kokarin ganin ta kawo dan wasan tsakiya na Norwich James Maddison 21 da mai tsaron baya na Fulham Ryan Fredericks, 25, domin maye gurbinsu a kungiyar.

Juventus tana da sha'awar ganin ta dauko dan wasan gaba na Kungiyar Chelsea Alvaro Morata sai dai tana buktarsa sane a takaitacen farashi

Mafi yawa daga cikin masu hanun jari a kungiyar Bordeaux's Sun ce baza'a sayar da dan wasan kungiyar Malcoma wannan shekarar ba duk da kasancewar wasu manyan kungiyoyin sun nuna sha'awarsu kan dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG