Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Ya Nemi Afuwa


Apple

Kamfanin Apple ya fito ya nemi afuwar abokan huldarsa bayan da ya sha suka kan rage saurin tsoffin wayoyinsa.

Biyo bayan kararraki da ya fuskanta da kuma suka daga abokan hulda, bayan da Apple ta fito ya tabbatar da cewa yana rage saurin tsoffin wayoyinsa dake da matsalar batiri. A makon daya gabata ne kamfanin Apple ya fito ya nemi afuwa wannan abu da yake.

Apple ya ce zai rage kudin batirin wayoyinsa ga masu bukatar canzawa, kuma zai canza manhajar wayoyinsa da zata rika nunawa a wayoyin iPhone idan baturinsu na da kyau.

Masu amfani da wayoyin kamfanin Apple sun dade suna zargin kamfanin da regewa tsoffin wayoyinsa inganci ko sauri, a duk lokacin da yake dab da fitar da sabuwar wayar iPhone, don tilastawa masu amfani da wayoyin sayen sabbin wayoyin da ya fitar.

Apple dai ya fuskanci kararraki har kashi biyu a Amurka kan cewa yana yaudarar masu amfani da wayoyinsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG