Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Baiyana Murna Da Bukatun Su A Sabuwar Shekara


DandalinVOA na yi wa daukacin al’umma murnar sabuwar shekara ta 2018 wanda akan haka ne muka samu zantawa da wasu matasa dangane da bukatun da suke so su cimma tare da kudororinsu a wannan shekara ta 2018.

Abdukarim Buyaya, matashi ne kuma ya ce babban burinsa a wannan sabuwar shekara shine ya mallaki mota sa’annan yana fata Allah ya bashi damar yin aure, da kuma dai-daitar lamura a kasa baki daya tare da fatan shugabani zasu sakar wa marasa galihu dama domin a dama da su.

Shi kuwa Buhari Fagge babban burinsa bai wuce ya tsinci kansa yana aiki a gidajen jaridar kasashen waje ba.

Fatima ita kuwa fatan ta shine farashin komai ya sauka sa’annan tana da burin gyara wasu hallayen ta tare da fatan cikawa lafiya.

ku biyu mu domin jin wannan da ma wasu kudorori na matasa, daga karshe dandali dai na fatan yi wa al’umma murna shiga sabuwar shekara tare da cimma bukatu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG