Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Na Bukatar Karin Kudi Masu Yawa A Manchester


Kocin Manchester united José Mourinho na bukatar Karin kudi masu yawa a Manchester United don shiga sabuwar kwangila da kungiyar

Mourinho yace yana da niyyar sanya hannu don karin kwantiraginsa a Manchester United, amma zai yi hakan ne kawai domin ya yi imanin cewa ya cika sharuddan da zai iya nunawa na nasarorin da ya samu a kulob din da halin da ake ciki a yanzu.

Mourinho yana daukan kimanin fam miliyan £15 a duk shekara, amatsayin albashi,

Kocin ya kusa kai rabi cikin kwantiragin shekaru uku da ya amince da shi a shekara ta 2016. A farkon kakarsa ta United Mourinho ya lashe kofi biyu, na EFL Cup da Europa League.

Ya kuma sami nasarar kai kungiyar zuwa gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) 2017/18 .

Kuma kungiyar ta Manchester united ce ke Jan ragamar rukunin (A) da maki 6.

Haka kuma Manchester united tana mataki na biyu a saman teburin Firimiya lig na bana a wasanni takwas da ta fafata da maki 20 duk a karkashin jagoranci José Mourinho.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG