Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Rashin Dan Wasan Kwallon kafa


 Gianni Infantino
Gianni Infantino

Dan wasa mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta Persela Fc, dake kasar Indunisiya mai suna Choirul Huda ya mutu yayin da suke wasa da kungiyar Semen Padanga, a wasan lig na bana.

Hatsarin ya afku ne ranar yayinda mai tsaron ragar sukayi karo da wani dan wasa nan take ya fadi, inda akayi kaishi Asabiti,Likitan kungiyar mai suna Andri Nugroho, ya bada tabbacin mutuwar mai tsaron ragar Choirul.

Choirul dan shekaru 38, da haihuwa an haifeshi ranar 2/6/1979 a wani gari Lamongan dake kasar Indunisiya, ya dai fara wasan kwallon kafarsa ne a 1999, a kungiyar Persela Lamongan, kuma ya kare a wajan dan wasan ya samu shiga wasanni har 503, a kungiyar.

Dubban magoya bayan kungiyar na Persela ne suka nuna juyayunsu na mutuwar dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:11 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG