Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hana Mawaki Aure Saboda Sana'a


Al- Amin Yahaya Sulaiman
Al- Amin Yahaya Sulaiman

Wani matashin mawakin Kannywood, Al Amin Yahya Sulemanyace wakokinsa sun fi karkata abisa hadin kan matasa ta fuskar aure ganin yadda hakkan ke tattare da matsalolin daban daban mussamam na bambance-bambancen kabila.

Aminaz kamar yadda ake kiransa ya ce dalilin kasancewarsa hana shi aure a lokacin da yana nemi wata yayi tasiri a dalilin nau’in wakar da yake yin a batun aure.

Ya kara da da cewa kasancewarsa mawaki, yasa aka hana shi saboda fasarar da ake wa sana’ar waka da mawaka, wanda wannan na daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta a wajen neman aure.

Ya kara da cewa yana son nusar da al’umma muhmmanci hadin kai da son juna, a cewarsa dukkanin hallitu daya suke a wajen ubangiji.

Wakarsa ta na kuma nusar da matsalolin bayan aure na karya tsakanin ma’aurata ta fannin kabila ko bambanci rayuwa kafin da bayan aure.

Aminaz ya ce wakarsa tana kara nusar da ire-iren wasu sana’oi da ake rainawa ko ba’a amince da su ba a cikin al’umma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG