Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hattara Rage Buri Da Kwadayi Mata


Halima Ibrahim Yusuf
Halima Ibrahim Yusuf

Wata matashiyar jaruman Kannywood, Halima Ibrahim Yusuf, ta bukaci mata su rage dagawa da jiji da kai da kuma rage kwadayi wajan harkokin yau da kullum masamman wajan batun aure.

Tace daya daga cikin dalilan da ya sa ta shiga harkar fina finai shine domin ta isar da sakonnin da suka shafi mata, musammam yadda ya kamata iyaye su dinga sanya idanu akan harkokin da ya shafi ‘ya’yan su na yau da kullum.

Jaruman ta bayana haka ne a wata ganawa da tayi da Dandalinvoa. Ta kara da cewa ta dade tana bukatar shiga masan’antar amma sai daga baya bayan da ta kammala karatun ta na jami’a sannan ta samu yardar iyayenta na shiga masana’antar.

Ta ce sha’awa da irin wa’azantarwa da fina-finai ke yi wa alumma, ta harkar zamantakewa da harkokin yau da kullum yan taka rawar gani a rayuwar jama’a.

Ta kara da cewa daga cikin wasu fina-finan da ta yi a halin yanzu akwai na nusar da mata rage buri da kwadayi wajen aure.

Halima ta kara da cewa tana burin, ganin cewa al’umma su amfana da irin darusa da ke kunshe a cikin irin fina finai, da suke gabatarwa domin alumma su amfana da irin nata gudunmuwar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG