Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Fara Amfani Da Gidajen Silima A Kannywood


Hafizu Bello Kannywood
Hafizu Bello Kannywood

Malam Hafizu Bello, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Kannywood, yace masana;antar ta fito da Kannywood, Box-office domin hawa turban da duniya ke bi wajen nuna fina-finai a gidajen kallo na silima kafin lokacin da zasu fito kasuwa a faifai.

Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewar jihar Kano, na da kimanin gidajen kallo guda dubu daya,(1,000) wanda da ake san ran amfani da su wajen nuna sabbin fina-finai kafin a fitar dasu kasuwa akan faifai.

Hafizu Bello ya ce sun fara gwaji a karamar Sallar, da ta gabata inda suke hango wasu matsalolin da yakamata su magance da kuma inganta inda ya kamata a inganta, tare da cewar ana sa ran fara shirin gadangadan a karshen wannan wata.

Ya kara da cewa tsarin zai kasance tsakanin ‘yan kasuwa wadanda suke shirya fim, da gidajen kallon da masu shirya Box office wajen bada kaso ga kowa.

Yana mai cewa dalilin rashin kasuwa da kuma masu satar fasaha ne da kuma kwaikwayan yadda lamarin yake a fadin duniya ya sa masana’antar daukar wannan matakin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG