Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bana Babu Harka Ga wasu Jaruman Bollywood


 Shah Rukh Khan
Shah Rukh Khan

Shah Rukh Khan da Salman Khan, jarumai ne a Bollywood, da suke taka rawar gani a faggen fina finai, amma a wannan shekarar na 2017, kawo yanzu fina finan su basu taka rawar da suka saba takawa ba a masana’antar Bollywood.

Daga farkon shekarar damuke ciki kawo yanzu banda fim din Baahubali, babu wani fim din Indiya, da ya samu fiye da dalar Amurka miliyan ashirin da hudu $24M, a Bollywood.

Fim din Raees’ na Shah Rukh Khan, ya samarda kusan dalar Amurka miliyan ashirin da biyu $22M, amma ganin abinda aka kashe wajan hada fim din za a ce har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Abinda yafi tadawa Shah Rukh Khan, hankali a wannan shekarar shine rashin tabuka abin a zo a gani da fim dinsa na Jab Harry Met Sejal, yayi ganin cewa da rarrafe fim din ya samu dala Amurka miliyan goma $10M.


​Itama jaruma Kangana Ranaut, fina finan ta Rangoon da Simran basu samarda abinda aka sata ba amma Akshay Kumar, ya samu darawa domin kuwa fina finansa Jolly LLB 2. da Toilet –Ek Prem Katha sun karbu hanu biyu biyu a Bollywood.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG