Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Bukatar Gwabzawa Da Jamus


Gernot Rohr
Gernot Rohr

Babban mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa na Super Eagle, Gernot Rohr, ya shedawa hukumar kwallon kafa ta Najeriya cewa yana da bukata hukumar ta shirya wasan kwallon kafa na sada zumunta tsakanin Najeriya da kasar Jamus, masu rike da kambin zakaran kwallon kafa na duniya.

Ya ce ya fadawa shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya cewa a yi kokarin shirya wasan sada zumunta da kasar Jamus, daga watan Nuwamba na bana zuwa watan Maris na shekarar 2018, ko kuma wata Mayu zuwa Yuni na shekarar 2018, idan har kasashen basu cikin rukuni daya.

Rohr, ya ce zai bukaci ayi wasan a babban birnin tarayya Abuja domin nunawa kasar ‘yan wasa ashirin da uku, 23, da zasu wakilci kasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kuma yin kasar bankwana akan haryarsu ta zuwa kasar Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG