Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Justin Bieber Ba'a San Mawaka Da Mugun Haliba:Inji Wata Mai-Kaunar Shi


Matashin Mawaki Justin Bieber

Biyo bayan wani taron masoya da aka gabatar, a bakin wani katafaren otel, daga saukar shi, shahararren matashin mawakin Amurka Justin Bieber, ya kara nuna mugun halin shi na kin magana da masoyan shi.

Wata matashiya masoyiyar shi ta bukaci da su dauki hoto, amma ya ki yarda da hakan, wanda har ya maida mata da bakar magana. Inda yake cewa 'ki dubi matakin girmamawan ki' wannan wani mugun hali ne aka san matashin mawakin da shi.

Matashiyar ta roke shi da cewar tana son yin hoto da shi, amma bai aminta ba, wannan bashine karo na farko da yayima masoyan shi haka ba, mussamman ‘yan-mata. Wasu na ganin kamar tun matsala da ya taba samu, da tsohuwar budurwar shi Selena Gomez yasa baya kaunar 'yan-mata

Matashiyar Sebah Helal, mai shekaru ashirin, tace gaskiya abun da yayi mata, shine cin zarafi na karshe, domin kuwa har mahaifiyar ta, na gaya mata cewar ya wulakanta ta. Bayan kwashe awowi suna jiran shi ya fito daga otel din shi, amma yana fitowa sai yayi musu wulakanci.

A ‘yan watanin baya mawakin ya bayyanar a shafin shi na instagram da cewar, kada wani masoyin shi ya sake ganin shi, a kan hanya yace yana bukatar daukar hoto da shi, don ya gama daukar hoto da mutane.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG