Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Na Iya Fuskantar kora


Wani kamfanin cacar wasanni yayi hasashen cewa a yanzu haka, manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Jose Mourinho, shi ne na biyu a cikin manajojin kwallon kafar dake bugawa a Firimiya Lig wadanda suka fi fuskantar kasadar cewa za a kore su daga kan kujerun su.

Kamfanin na Betfair Sportsbook, yace manajan kungiyar Sunderland, Dick Advocaat, shine kawai ya ke gaban Mourinho a cikin masu kasadar rasa ayyukansu.

Wannan yana zuwa ne a bayan da kungiyar Manchester City ta lallasa Chelsea, mai rike da kofin wasannin lig-lig na firimiya a yanzu haka, da ci 3 da babu a ranar lahadi.

Kafin wasan na ran lahadi ma, Mourinho ya fuskanci suka sosai a saboda rage darajar da yayi ma likitar Chelsea, Eva Carneiro, a bayan da ta duba lafiyar Eden Hazard ana gaba da tashi daga wasa kunnen dokin da suka yi da Swansea ranar asabar ta wancan makon.

Kamfanin Betfair yace idan har Mourinho bai san yadda yayi kungiyar Chelsea ta fara lashe wasanni cikin ‘yan makonnin da suke tafe ba, to tana yiwuwa yana kan hanyarsa ta barin Stamford Bridge, duk da cewa a cikin wannan watan ya sanya hannu a sabon kwantaraki na tsawon shekaru 4.

Wani masanin tamaula na Betfair yace ‘yan wasa zasu ci gaba da nuna goyon baya da mubaya’a ga Mourinho a yanzu, amma idan har Chelsea ta ci gaba da shan kashi a wasanni 4 zuwa 5 masu zuwa, to abubuwa zasu fara warware masa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG