Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Fim Ya Zama Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai


Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu
Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu

Gwamnatin jahar kano ta nada wani daga cikin 'yan fim a matsayin shugaban hukumar tace fina finan Hausa, Isma'ila Na Abba wanda aka fi sani da lakabin Afakalla, shine shugaban kungiyar masu shirya fina finai ta arewacin Najeriya reshen jahar Kano.

Ismaila Afakalla, tsohon mai shirya fim din Hausa ne, kuma yana fitowa a wasu fina finai, ya na kuma bada umurni.

ko da shike wanna shine karo na farko da gwamnatin jahar ta nada daya daga cikin 'yan fim domin rike irin wannan mukami, abin tambaya anan shine, shin me gwamnatin ta gani wanda ya sa ta nada daya daga cikin 'yan fim din domin jagorantar wannan hukuma?

A shekarun da suka gabata, jahar kano ta kai 'yan fim din Hausa da dama gidan yari a sakamakon rashin bi ko karya wasu dokoki.

Bayyana ra'ayin ka/ki akan shafin mu na facebook.com/dandalinvoa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG