Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsegumin Wannan Makon Na Kannywood


2201858 - Gossip men
2201858 - Gossip men

A fannin tsegumi kuwa yanzu haka dai mawaki kuma jarumi Adamu Hassan Na Gudu, bashi da na biyu ta bangaren gayyata da yake samu wajen nishadantarwa a bangaren manyan bukukuwan aure, a fadin Najeriya da ketare. A dai makon da muke bankwana da shi ne Adamun ya samu gayyata a garin Bauchi don gudanar da wasan bikin aure.

Jarumar fina finan Hausa Rahama Sadau tace, ta fara fitowa a fina finan kudancin Najeriya da akafi sani da Nollywood, domin ta inganta tare da samun karin ilimi kan sana’arta, sai dai tace bazata taka wata rawa ba da zata sabawa addini ko al’adar ta ba.

A jiya Juma’a ne dai aka fara nuna fim din ‘Gwaska’ a cinimar Ado Bayero Mall dake Kano, an dai nuna Fim din ne sau uku a jiya wanda akayi kallon tare da jarumin wato Adam A Zango.

XS
SM
MD
LG