Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsegumin Wannan Makon Na Kannywood


2201858 - Gossip men
2201858 - Gossip men

A ranar Asabar din data gabata ne akayi addu’ar kwana bakwai na mahaifin sharifin mawaki Sani Sidi Sharifai, dafatan Allah ya ji kan magabatan mu tare da saka musu da gidan Aljanna.

Ranar litinin ‘din da ta gabata ne mahaifiyar mawakiya Aisha Golden Goose ta riga mu gidan gaskiya.

A ranar asabar din data gabata ne kuma basaraken jarumi Adam A Zango, ya rubuta a shafin sa na Instagram cewa, ya daina fitowa a duk wani fim da ba’a shirya kashe kudi sama da Naira miliyan biyu ba.

Wasu ‘dalibai a jami’ar Bayero ta Kano sun rubuta Makala ta karshen karatun su akan wakar Adam A Zango mai suna Gumbar Dutse.

Jiya Juma’a ne jaruma Rahama Sadau ta fara aikin wani fim na ‘yan kudu wato masana’antar Nollywood, jarumai dai zatayi aiki tare da manyan jaruman Nollywood.

XS
SM
MD
LG