Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Sabon Shugaban Kasar Najeriya


Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace babu yadda za’a yi Najeriya ta yi ikirarin samun nasara akan mayakan Boko Haram, har sai an ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace daga makarantarsu ta sakandare dake Chibok a watan Afrilun shekarar da ta gabata.

A jawabin da yayi bayan rantsar da shi yau Juma’a, Mr. Buhari yace dole ne a ceto daliban Chibok wadanda mayaka suka yi awon gaba da su a Jihar Borno. Sabon shugaban ya kira Boko Haram a matsayin wata kungiya mara Imani da rashin Allah a zuciyarta, kuma ta nisanta matuka daga addinin Musulunci.

Buhari wanda ya karbi ragamar mulki daga Goodluck Jonathan shine dan Najeriya na farko da ya kada shugaba mai ci a zaben jefa kuri’a. Ya dauki rantsuwar kama bakin aiki a lokacin da ake gudanar da bukukuwa a birnin tarayyar Najeriya Abuja, dake kewaye da hotuna da kyallaye launukan fari da ruwan ganye, wato launukan tutar Najeriya.

A jawabinsa na farko, Mr. Buhari yace yana son Najeriya ta taka rawar gani a jagorancin shugabanci a nahiyar Afirka baki daya. Najeriya tafi kowace kasa a nahiyar yawan jama’a, kuma itace kan gaba a hako danyen mai a duk fadin Afirka.

Sabon shugaban ya amince cewa kasar na cikin matsalolin tattalin arziki, a ciki harda matsanancin rashin ayyukan yi da bakin talauci, kuma yayi alkawarin takalar matsalar rashin wutar lantarki nan take.

XS
SM
MD
LG