Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Zata Koma Maiduguri


Alokacin jawabin sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan an rantsar da shi, ya ce idan har ana so a shawo kan matsalar Boko Haram, sai shelkwatar sojin kasar ta koma Maiduguri, babban birnin Jahar Borno.

Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, y ace shelkwatar sojojin kasar dake Abuja, babban birnin kasar, za ta yi kaura zuwa Maiduguri domin a kawo karshen matsalar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square bayan da ya karbi ragamar mulki a matsayin sabon shugaban Najeriya.

Najeriya, musamman ma a yankin arewa maso gabashin kasar, ta kwashe kusan shekaru shida tana fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane kana sama da miliyan suka bar muhallansu.

XS
SM
MD
LG