Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Wasu Matasa Masu Yankan Kai


Rundunar ‘yan Sandan jihar Neja, ta cafke wasu matasa biyu gawurtattun matsafa da kan wani yaro mai shekaru takwas (8) da haihuwa.

Matasan Abdulrashid Aminu, shekaru 22, Ismaila Mohammed shekaru 27, an cafke su ne akan hanyar Minna zuwa Paiko, a lokacin da jami;an ‘yan Sandan ke gudanar da wani bincike na masamman.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda DSP Babalola, Olanrewaju Adewole, wanda ya tabbatar da labarin ya ce nasarar da aka samu na cafke matasan ya biyu bayan bibiyan su da jami’an suka jima suna yi.

Ya kara da cewa matasan sun kware wajan yankan kai domin yin tsafi, yana mai cewa yaro da suka kashe sunan sa Hassan Abubakar, dan kauyen Bakajeba dake cikin karamar hukumar Paiko, a jihar ta Neja.

Kakakin ‘yan Sandan ya ce matasan da ake zargin sun amsa laifin aikata wannan aika aikan. Shi dai yaron tun ranar ranar Asabar ya bace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG