Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaddawalin Zagaye Na 16 A Gasar Europa League 2016/17


A cigaba da gasar cin kofin Turai Europa League 2016/2017 zagaye na 32, karo na biyu jiya kungiyar Osmanlispo, ta sha kashi daci 3-0 a hannun Olympiakos.

Apoel ta doke Athletic club daci 2-0, Roma 0-1 Villarreal, Ajax 1-0 Legia Warsaw, Besiktas ta sha Hapoel Be'er Sheva 2-1, Zenit nada 3 Anderlecht 1.

Shakhtar ta sha kashi a hannun Celta Vigo, kwallo 2-0, Florentino 2-4 Borussia Monchenglabach, Lyon ta lallasa AZ Alkmaar da kwallaye 7-1, Kobenhanv ta yi canjaras 0-0 tsakaninta da Ludogareth, Sparta Praha ta yi kunnen doki 1-1 da FK Rostov, Genk ta samu nasara akan FC Astra Giurggiu da ci 1-0.

Bayan kamamala wasan an fidda jaddawalin kungiyoyin da zasu kara da juna a zagaye na Goma sha shida Quarter final Kamar haka;

Celta Vigo da Krasnodar

Apoel da Anderlecht

Schalke 04 da Borussia Monchenglabach

Lyon da Roma

FK Rostov da Manchester united

Sauran sune;

Olympiakos da Besiktas

KAA Gent da Genk

Sai Kobenhanv da Ajax

Za'a buga wasanninne ranar Alhamis 9/3/2017, inda za'a suke karawa a karo na biyu ranar 16/3/2017.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:30 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG