Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juventus Na Da Kwarin Gwiwar Lashe UCL 2016/17 (Gonzalo Higuian)


A jiya kungiyar kwallon kafa ta Bayern Leverkusesn, ta sha kashi a gidanta a hannun Atletico Madrid, da ci 4-2 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai UCL 2016/2017 a matakin zagaye na Goma Sha shida.

Ita kuwa Manchester City, ta kwaci kanta dakyar a hannun Monaco da kwallaye 5-3, a ranar laraba 15/3/2016 kuma, zasu sake fafatawa a karo na biyu.

A yau kuma Sevilla, zata karbi bakuncin Leicester city, a gasar zakarun turai na shekara 2016/2017, ita kuwa FC Forto, zasu barje gumi da Juventus, za'a buga wasanne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.

Danwasan Juventus, Gonzalo Higuian, yace yana da kwarin guiwa kungiyarsa ta Juventus, zata lashe gasar zakarun nahiyar turai na bana 2016/2017.

Shi kuwa Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Sevilla, Vicente Iborra, yayi kira ga takwarorinsa ‘yan wasan Sevilla, ne da suyi taka tsan-tsan a wasan da zasu yi yau da Leicester city.

Iborra, yace domin Leicester, ba karamar kulob bace a shekarar 2015/2016 ita ta lashe gasar firimiya lig na kasar Ingila, dan haka ya zamo dole su zage damtse ganin sun samu nasara a wasan.

Leicester city dai a Bana bata tabuka abun azo aganiba a bangaren Firimiya lig na kasar Ingila domin tana mataki na sha bakwai ne da maki 21 a wasanni 25 da ta buga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG