Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Theo Walcott Ya Jefa Kwallonsa Ta 100 A Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal


A wasan da aka buga na cin kofin kalu bale FA Cup na shekarar 2016/2017 a kasar Ingila, A jiya Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasarar hayewa zuwa zagaye na kusa da na kusa da na karshe bayan ta doke Sutton United daci 2-0.

Don haka Arsenal zata kara da Lincoln City a ranar Asabar 11/3/2017, haka kuma dan wasan Arsenal, Theo Walcott, ya jefa kwallonsa ta dari a Kungiyar bayan ya shafe sama da shekaru Goma yana fafatawa a kungiyar.

Walcott ya kafa tarihinne a wasan da Arsenal, tayi da Sutton united, a daren jiya a gasar FA Cup 2016/2017. Walcott ya saka kwallo ta biyu a ragar Sutton, acikin minti 55 da fara wasan inda aka tashi 2-0.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG