Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Zata Kara Da Chelsea A Gasar FA Cup Quarter Final 2016/2017


Logo Manchester United
Logo Manchester United

A cigaba da gasar cin kofin kalu bale FA Cup na kasar Ingila na shekara 2016/2017, Kungiyar kwallon kafa ta Burnle, ta sha kashi a hannun Lincoln City daci 1-0.

Huddersfield Town, ta yi canjaras 0-0 da Manchester City, Millwall kuwa ta doke Leicester City da kwallo 1-0, Middle Brough na da 3 Oxford United, nada 2
Wolverhampton ta sha kashi a gidanta daci 2-0 a hannun Chelsea, Blackburn Rovers 1-2 Manchester United.

Yau kuma za'a kara tsakanin Sutton United, da Arsenal da misalin karfe tara saura minti biyar na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru.

Bayan kammala wasannin an fidda jaddawalin zagayen nakusa da na karshe Quarter final, Kungiyar Chelsea, zata kara da Manchester United, MiddleBrough tana jiran Huddersfield ko Manchester City, Tottenham da Millwall
Lincoln City kuwa tana jiran Sutton United, ko Arsenal
Za'a buga wasanninne tun daga ranar 10 /13 na watan Maris 2017.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:36 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG