Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jackie Chan Yayi Alkawarin Koya Wa Sonu Sood Harshen China


Jackie Chan
Jackie Chan

Da alamun shahararren jarumin fina-finai na China da makamantansu, Jackie Chan, ya shaku sosai da jarumin fina-finai na Bollywood, Sonu Sood.

Cikin kwanakin nan ne Sonu Sood ya kammala daukar nasa bangaren na wani sabon fim na Amurka mai suna "Kung Fu Yoga" tare da shio Jackie Chan a kasar Dubai. Stanley Tong shi ne darektan wannan sabon fim da ake dauka.

Kafofin labarai da dama sun ce a lokacin da yake shirin tashi don komawa kasarsa ta China, Jackie yayi ma Sonu alkawarin cewa zai koya masa harshen China a duk lokacin da ya kai ziyara can.

Haka kuma an ce Jackie ya ba Sonu kyautar wani littafin nasa a kan fim dinsa.

XS
SM
MD
LG