Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawa na Daga Cikin Al’adar Malam Bahaushe


Sanusi Oscar Kannywood
Sanusi Oscar Kannywood

A yau dandalinVOA ya samu bakwanci wani mai bada umarni Sunusi oska wanda aka fi sani da 442.

442 dai ya fara harka fim da bada umarni shekaru 20 da suka wuce ya kara da cewa sha’awace ta ja shi ga harkar fim kuma ya fara ne da bada umarnin wani fim mai suna Ummul Khairi.

Mal Sunusi dai ya ce bai karanci harkar fim ba amma ya halarci wasu bitoci da suka danganci fina-finai , 442 ya ce tun da ya fara harkar fim bai taba fitowa a wani fim ba ko a wani fannin na fim industry ba.

Dangane da batun raye-raye ya ce mutane ba a taba yi musu gwaninta ,ya kara da cewa sanya rawa da suke yi a fina finai su na yinsa ne domin shigar da sako a fina finansu.

A cewarsa rawa na daga cikin al’adar malam Bahaushe domin kuwa tun da can ana rawa a dandali.

A fannin tsegumi kuwa wasu jarumai na garin Zaria aikin wani fim da zai yi buda kan yadda malam Bahaushe ke gudanar da rayuwarsa a alummance.

XS
SM
MD
LG