Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaima Ka Dara!


Shirin kai ma ka dara ya ji labaru masu ban dariya ne daga wasu 'yan mata, inda ko wacce ta bada nata dan takaitaccen labarin domin nishadantar da ku masu sauraro.

Labari na farko ya yi magana ne akan wani asibitin masu tabin hankali da yake yunkurin sallamar wasu daga cikin mahaukatan a hasashen cewar ko sun sami sauki, dan haka sai aka ce to bari a gwada su!.

Sai malaman asibitin suka yi zanen kofa da hannun bude kofar a jikin bangon dakin aka ce masu to ga hanya can kowa ya fita, da jin haka sai mahaukata suka afka da gudu suna ruguguwar fita, sai daya daga cikin su ya zauna bai je ba.

Da malaman asibitin suka ga mutumin guda bai tashi ba sai suka ce kila shi kadai ne ya fi kowa lafiya sai aka tambaye shi, mala ya ka zauna? sai kawai ya budi baki ya ce duk basu da hanakli makullin kofar na nan hannu na!.

Labari na biyu kuma wani dan jarida ne zai wuce sai yaga jama'a sun taru a gefen hanya wato alamar an yi hatsari kenan, sai dan jaridar ya nufi wurin, da isar sa sai ya ji ana cewa aiko da alamu ta rasu, gogan naka sai ya kara azamar kutsawa domin ganewa idon sa abin da ya faru.

Ana cikin wanna hali sai wani mutum ya budi baki ya ce masa, haba malan me ya faru ne kake ta kokarin kutsawa? sai kawai ya budi baki ya ce ku tausaya mani domin wadda ta mutun nan baba ta ce, da jin haka sai hankalin jama'a ya karkata a kansa, ana bashi wuri sai yaga ashe tunkiya ce aka banke da mota!.

Saurari sauran labaran a nan.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG