Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwalliyar Burge Samari


A shirin mu na mata, yau wakiliyar dandalin VOA ta zanta da wasu ‘yan mata wadanda suka bayyana muhimmanci da tasirin kwalliya domin sub urge samarin su, ko sahike wasu sun ce akwai kwalliyar safe da kuma kwalliyar dare amm a a cewar su kwalliyra dare ta fi.

A cewar daya daga cikin ‘yan matan “gaskiya ina yin kwalliya amma na fi shi’awar yin kwalliya da daddare saboda komi muninka ba wanda zai gane musamman ko da na cika hoda a fuskata, sai inyi kyau in zama tamkar ‘yar tsana, duk sauraryin da ya ganni sai ya sake kallo na.”

A cikin irin kayan shafar da ‘yan matan kan yi anfani da su, sun hada da wani jan baki wanda ake kira Maja, budurwar ta kara da cewa akwai wani abu mai suna kwansela da fandeshan, da eye shado da sauran su. ta kara da cewa idan ta shafa su babu yadda saurayi zai gane cewar hoda ta shafa koda kuwa ta cika da yawa.

Wata daga cikin 'yan matan ta bada bayanin cewar idan ta yi kwalliyar ta je fati ko gidan biki, babu shakka sai ta fi amaryar kyau, kuma ta haka ne kawai budurwa zata yi kasuwa a wurin samari.

Saurari cikakken shirin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG