Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Makomar Kannywood In Ji Abdulkarim Mohammad


Abdulkarim Mohammad Kannywood
Abdulkarim Mohammad Kannywood

Shirinmu na nishadi a yau na mussamam ne domin kuwa mun sami wani jigo da ya shafe shekaru a masa’anatar yin fina finai na kannywood.

Ba wani ba ne illa Abdulkarim Mohammad wanda ya fara aikin talabijin da fina--finai tun 1979 inda ya ke cewa har yanzu masu harkar fim basu da cikakkiyar masaniya a harkar fim din da suke yi.

Abdulkarim Mohammad ya karanci Radio Television and Film production a degree na farko sannan ya karanci Print media a na biyu ya ce sha'awa ce da dama ta kawo shi ga harkar fim.

Ya kara da cewa ba wani da yake cikin jahilci da zai ce zai fadakar da alumma akan wani lamari da shi kansa bai gama fahimtarsa ba.

Ya ce mafi yawan mutanen da ke shirya fina-finai a yanzu sun fi maida hankali ne wajen abin da zasu samu maimakon fadada bincikensu kafin su fitar da fim.

Abdulkarim ya ce har yanzu akan samu kura kurai a wasu labarin fim da ake fitarwa, ta hanyar yin kuskuren sanya abubuwan zamani a cikinsu.

A fannin tsegumi kuwa Allah ya albarkaci iyalan edita fina-finai Rabiu Michu karuwar ya mace za’a yi radin suna a ranar labara.

XS
SM
MD
LG