Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Kira Ga Matasa Dasu Cire Son Zuciya A Siyasa: Danladi


Har kawo yanzu iyayen siyasa da suka ga jiya suka ga yau ne, su kai kane kane a siyasar Najeriya, inji wani matashi dan gwagwarmayar siyasa Danladi Mai Fata Sharada.

Ya ce manyan 'yan siyasa tunaninsu ya kare, Inda matasa a yanzu a wannan lokaci suke kan ganiyar tunanin cigaban kasa, sabanin iyayen 'yan siyasa da tunaninsu, da wayonsu da karfin ya kare basu iya wani kokari na cigaban kasa.

Babban abinda ke tauye matasa a yanzu mafi yawa akwai karanci ilimi, rashin sanin ciwon kai, wanda wadannan iyayen gidan 'yan siyasan ke amfani da damar sa matasan bangar siyasa, amfani da kwayoyi kai harma amfani da makamai wajen bangar siyasa.

Danladi yayi kira ga matasa da sucire son abin duniya daga zukatan su, da su tuna cewa manyan 'yan siyasa sun maida su kashin baya a cikin al’umma. Ya kuma kamata mu tashi tsaye domin mu samu madafan ikon a dinga basu damar damawa da su a harka ta demokaradiyya.

Ya ce suna fuskantar matsala ta karanci kudi da zai taimaka mu su wajen wayar da kan matasa illar amfani da su, da manya 'yan siyasa ke yi da su wajen ta’amali da miyagun kwayoyi tare, bayan sun tura 'yayansu kasahen waje domin karatu daga bisani su dare kujerun iko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:19 0:00
  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG