Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Sana’a Tace Ta Manhajar Whatsapp: Zulaiha Adamu


Zulaiha dai daliba ce wacce ta ce kananan sana’oi abu da ya wajaba ga mata mussamam ma duba da yadda rayuwa take a yanzu , kananan sana’oi na taimakawa wajen rufawa mata asiri.

Inda ta bayyana tana sayar da kayan yara da na mata kimanin shekaru biyu da suka wuce domin zama mace mai dogaro da kai, kuma ina wannan sana’ar ne ta hanyar amfani da kafar Whatsapp domin tallata hajjata a cewar matasiya malama Zulaiha Adamu.

Ina tallata hajar a manhajar idon mutane suka ga abunda suke bukata sukan yi Magana sai su aika da kudin su ni kuma sai aika masu kayan da suka zaba.

​Dukkan wani mai kananan sana’oi yakan fuskanci kalubalen kasuwa haka nima nasamu matsaloli amma duk da hakan bai sa na fasa sana’a ba.

Daga karshe malama Zaulaiha tayi kira ga mata dasu jajirce, wa wajen neman sana’ar hannu da zai dinga kawo musu kananan kudade domin kawar da kananan bukatu ba tare da sunyi dan murya ba wajen mai gida ko iyaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG