Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Hanyar Waka Nakan Isar Da Sakonni Masu Ma'ana


Na fara waka ne sakamakon wata waka da akayi ta mahaifiya, wanda hakan yasa nima nayi tunani yiwa mahaifiyata waka, akan irin dawainiyar da tayi da ni, kamar yadda mawaki Usman Suleman Aliyu wanda aka fi sani da Shamaki Young Moller.

Mawakin Raggea da hip hop wanda ya ce waka wata hanya ce ta Nishadi, da ilimantarwa a lokaci daya, ya fara da wata waka mai suna Halima wanda ya rera bayan yaje neman aure aka hana shi da wannan al’amari ne ya fara.

Nakan isar da sakonnin ga matasa da akan matsalolin fyade da shaye-shayen kwaya, da sauran matsaloli da matasa kan tsinci kansu a ciki. Shamaki dai kamar sauran mawaka ya fita daban domin yana rera wakoki daban daban.

Shamaki ya kara da cewa ya fuskanci kalubale sosai kasancewar, shi dalibi ne, rashin kudi na daga cikin manyan abinda ke ci ma harkar wakar tuwo a kwarya, Inda yake cewa har akwai wani lokaci da aka taba bashi kudi yayi waka, amma ya kashe kudin bayan hakan ne ma ya shiga halin kaka ni kayi.

Amma duk da haka bai hanashi zage damtse ba, akan samun nasara bisa abunda yake muradi wato waka. Hakan yasa dai yana kira ga matasa da su guji shaye-shaye, da kuma kokarin samar ma kansu abunyi a duk lokacin da suka rasa aikin yi.

Sana'ar waka na taima mishi matuka wajen ganin ya tsare ma kanshi lalurorin yau da kullun, batare da yaje roko ko karamar muryaba. Haka kuwa wani abune da duk matasa ya kamata su maida hankalin su akai, musamman yanzu da siyasa ke kara kunno kai, kada su bari 'yan siyasa suyi amfani da su wajen tada zaune tsaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:27 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG