Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Su Kasance Masu Tawakali - Babban Sakon Suazo


David Samson Hassan
David Samson Hassan

Babban sakona a kullum shine mutane su kasance masu tawakali akan duk abinda Allah ya basu su dangana da Allah ne ya basu ba mutum ba, haka kuma su kasance sun kauracewa gadara da fadin rai, inji mawakin reggae David Samson Hassan wanda aka fi sai da David Suazo.

Suazo ya bayyana cewa ya koyi kidan jita a wajen wani mawaki da ake kira brother Raymond London, matashin ya kara da cewa a wasu lokutan jama’a na yi masu kallon marasa aikin yi kuma marasa da’a.

David ya bayyana cewa yakan fadakar da al’umma cewar waka wata hanya ce ta isar da sako ta yadda zai ratsa zuciyar mutune cikin sauki da annashuwa ba tare da an tursasa su ba, kuma duk a lokaci guda a wa’azantar da su.

Daga karshe matashin ya bayyana cewa “ni mawakin Raggae ne wanda ke isar da sakonni ta hanayar waka tare da nusar da al’umma su zama masu dogaro da kansu a rayuwa ba tare da sun kwaikwayi rayuwar wasu ba”.

“Ni ba kamar sauran mawaka bane domin ina gudanar da ayyukana ne a cikin dakina, na rubuta wakata na karanta tare da kada jita da kaina kuma a hannu guda ina karatu na”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG