Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amitabh: Labarin Malamin Makaranta Da Ya Kafa Kungiyar Kwallo Da Zauna Gari Banza


Shahararren dan wasan kasar Indiya Amitabh Bachchan, ya shirya tsaf domin fara gudanar da ayyukan hada wani sabon fim a watan Oktoba na wannan shekara da muke ciki, kuma ana kyautata zaton zai ci gaba da taka rawar da ya kamata a fim din ba kakkautawa da zarar ya kammala ayyukan dake gaban sa.

Jarumin ya bayyana jin dadinsa musamman yadda ya zabi Nagpur, domin a cewar sa a nan wannan labara da za a shirya fim a kanasa ya samo asali, kuma ya kara da cewa daukar wannan fim a garin zai fi nuna manufar sa ta zahiri.

Daraktan da zai bada umurni a fim din ya bayyana cewa aiki tare da Amitabh mai shekaru 75, a duniya wata gagarumar nasara ce, ya kuma kara da cewa “Amitabh ya dade yana burgeni, shine gwani na, dan haka aiki tar da shi a wannan fim zai matukar kyau”.

Za a shirya fim din ne bisa rayuwar wani malamin makaranta da yayi amfani da matasan unguwa masu gararamba akan layuka wajan kafa kungiyar wasan kwallon kafa.

Ana kyautata zaton tsayin fim din zai kai minti 70 zuwa 80, inda Amitabh, zai kwashe kwananki 45 kai tsaye a Nagpur, kuma an shirya matasan da zai shirya fim din dasu sun shirya tsaf inda zai gana da sun a kwanaki biyu zuwa uku kafin a fara shirya fin din.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG