Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tiger Sharoff Zai Fito A Fim Din Hollywood Baya Ga Na Bollywood


Tiger Sharoff
Tiger Sharoff

A cewar rahottoni daga jaridar Mumbaiu Mirror, Lawrence Kasanoff, wanda shi ne ya bada umurni a fim din Mortal Kombat, ya kai ziyara babban birnin Mumbai don haduwa da Tiger, su tattauna a kan abinda sabon fim da zai shirya ya kunsa.

Ana sa ran cewa fim din na fada ne, Lawrence tare da shahararen marubuci da ya sha samun lambar yabo ta Emmy Sean Catherine Derek, da ya rubuta fim din Batman tare suka ziyarci Mumbai. Sanjay Grover, fittacen dan fim din Indiya Guslshan Grover, na ta aiki tare da 'yan Hoolywood tun shekarar bara kan sabon fim din.

Rahotonni sun bayyana cewa Sanjay ne ya bada sunnan Tiger ga masu shirya fina finan Hollywood din. Baya ga haka rahotonni sun nuna cewa Larry ya nuna wa Sanjay litafin sabon fim din daga bisani shi Sanjay ya bada shawarar cewa mai zai hana ya nuna sabuwar fuska a fim din yayinda da kuma ya bada sunnan abokin sa Tiger wanda suka girma tare suka kuma yi karatu tare.

Larry da abokan aikinsa sun yi na’am da Tiger, saboda tunnanin su na cewa yana da fuskar fitowa a fina finan turai, kuma ya iya fadan Martial Arts, haka kuma yana da mabiya da masoya sosai sa'an nan yana da kuruciya.

A da chan baya Sanjey yayi aiki a matsayin darakta, wa kamfanin fina finan Hollywood, na Metro Goldwyn Mayer (MGM) har na tsawon gwamman shekaru kuma ya sha taka rawa a cikin fina finan Hollywood kamar su The Hobbit, The Zookeeper, Fame, Creed, da wasu fina finan James Bond. Idan aka samu nasarar tabbacin shirya sabon fim din, toh Tiger na iya fitowa a ciki yana fada da Jackie Chan, Chuck Norris da Shannon Lee 'yar shahararren dan fim da aka sani da Bruce lee.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG