Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Saki Hotunan Jaruman Da Zasu Fito A Fim Din Thugs Of Hindostan


Gabbanin fitowar daya daga cikin manyan fina finan Indiya na wannan shekara ta 2018, ‘’Thugs of Hindostan’’, wanda zai fito a ranar zagayowar haifuwar Yash Chopra, za’a a gabatar da shahararrun jarumai kamar su Amitabh Bachchan, Amir Khan, Fatima Sana Shaikh, Aamir Khan da Katrina Kaif ga masoyan su.

An shirya fara nuna sabon fim din Thugs of Hindostan inda ake tunanin cewa za a gabatar da Amitabh Bachchan da Aamir Khan ranar 27 ga watan nan na Satumba wanda zai zo dadai da ranar zagayowar haifuwar Yash Chopra. An shirya nuna hotunan waddanda zasu fito cikin fim din da suka hada da katrina kaif da Fatima Sana Shaikh.

Fim din zai nuna ‘yan wasan su hudu a matsayin barayi waddanda suke tawaye da wani dan wasan da ake cewa Raj a fim, ganin kamannin waddanda za su fito a fim din ita ce hanya mafi kyau da zata jawo hankalin jama’a, a cewar wani dan kasuwa.

Za’a fara nuna kamanin ‘’Big B’ wato Amitabh sai na Aamir Khan, Katrina da Fatima, ko wane hoton dan wasa da za a nuna zai bada bayanin matsayin da dan wasan zai fito a fim din sai Katrina Kaif yayinda da ake daukan ta tana waka.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG