Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Waka Ne Domin Fadakar Da Matasa Illar Kwaya: Aisha Arewa


Aisha Muktar Rijiyar Lemo wacce akafi sani da Aisha Arewa, na fara waka ne bayan da na lura cewar kananan yara suna harka ta waka mussaman ma wakokin fina-finai, wanda tun da farko na fara da kasida a makaranta daga bisani sai na fara sauya akalar wakar tawa zuwa na nishadi da fina-finai.

Ta ce baya ga kasida da wakokin fina-finai, tana wakokin da suka danganci fadakarwa da wa’azantarwa, misali akwai lokacin da ta je gidan biki ta iske wata matashiya da take shan kwaya har ta kai ta ga matakin rasa masoya.

Aisha Arewa ta kara da cewa, wannan na daya daga cikin dalilan da yasa tayi sha'awar yin waka akan illiah kwaya, domin ta fadakar dasu ta hanyar nishadi.

kuma har ila yau, tana fadakar da illar yawan son 'yaya da matsalolin da hakan ke haifarwa, mussaman duba da yadda a yanzu iyaye ke nuna soyayya ga 'yayan su wanda haka yakan sa su kauce wa hanya mai kyau.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:05 0:00
  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG