Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hon Dogara Zai Taimaka Wa Matasa ‘Yan Kwallo A Jihar Bauchi


Hon Dogara
Hon Dogara

A ranar Juma'a da ta gabata 29/12/2017 aka buga wasan karshe na gasar cin kofin mai girma kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya Rtd Hon Yakubu Dogara, wanda aka sa a yankin Bauchi ta kudu mai taken (Unity Cup) karkashin jagorancin Pastor Ishaya Mags.

Kungiyoyin kwallon Kafa goma sha shida ne da suka fito daga kananan hukumomi daban daban na yankin Bauchi ta kudu suka fafata a gasar. An buga wasan karshe ne a lokacin da Hon Dogara, yake murnar cika shekaru 50 da haihuwa a duniya.

Tsakanin kungiyar kwallon Kafa ta 3sc Fc, dake karamar hukumar Bauchi da spreader Fc, na karamar hukumar Dass.

Kungiyar 3sc Fc, ce ta samu nasarar lashe gasar da ci 1-0 inda ta samu kyautar kudi Naira dubu dari #750,000 sai Spreader Fc, ta sami dubu dari #500,000 a mataki na biyu.

Boi United Fc, da ta fito daga karamar hukumar Bogoro, ta sami kyautar dubu dari #300,000 a mataki na uku. Fenerbahc Fc, kuma ta sami dubu dari #150,000 a mataki na hudu.

Bayan kammala gasar, Rtd Hon Yakubu Dogara, ya yi alkawarin taimakawa matasa masu shi'awar kwallon Kafa a jihar Bauchi, domin samun shiga cikin ‘yan wasan kwallon Kafa ta Najeriya, da kuma wasu manya-manyan kungiyoyin kwallon Kafa dake fadin kasar, har ma na kasashen duniya.

Ya kuma yi alkawarin sake shirya wani gasar wadda zata kunshi jihar Bauchi gaba daya tare da Kafa tasa kungiyar.

Wasan karshe ya gudana ne a karamar hukumar Bogoro, mahaifar Kakakin majalisar, wanda ya sami halartar ‘yan majalisar tarayyar Najeriya, da suka fito daga wasu sassan kasar ciki har da Hon Ahmed Yarima Misau, mai wakiltar Dambam, da Misau dake jihar Bauchi a majalisar wakilai dake birnin taraiya Abuja.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG