Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Saye Da Sayarwar 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A yayinda da kungiyoyin kwallon kafa na duniya suka kammala wasannin lig lig na kasashe daban daban, yanzu hankali ya karkata wajen saye da sayarwar 'yan wasa inda Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £50 don ganin sun sayo danwasan gaba na Lyon, Alexandre Lacazette, da alkawarin zata rika biyansa fam dubu 200 duk sati.

Real Madrid, ta shiga sahun neman matashin danwasannan Mbappe, dan shekara 18 da haihuwa daga kungiyarsa ta Monaco, Kungiyoyi da dama na kasar Ingila na sha'awar danwasan.

Liverpool ta ware fam miliyan £52 don ganin ta dauko danwasan Real Madrid James Rodriguez, dan shekara 25. Manchester United na dab da sayen danwasan gefe na Inter Millan, mai suna Ivan.

Romelu Lukaku, na Everton yace har yanzu bai fidda matsayarsa ta kungiyar da zai koma ba inda kungiyoyin kwallon kafa da dama ke sha'awar danwasan cikinsu harda tsohon kulob dinsa na Chelsea.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG