Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cheikh Tiote Ya Fadi Ya Mutu A Filin Wasa Yau Litinin


Cheikh Tiote
Cheikh Tiote

Tsohon dan wasan Newcastle United a Ingila, kuma mai buga ma kasarsa ta Ivory Coast tamaula, Cheikh Tiote, ya fadi ya mutu a filin wasa na sabuwar kulob dinsa a kasar China lokacin motsa jiki (training).

Wakilin dan wasan kasar Ivory Coast, kuma tsohon dan wasan Newcastle United da ta samu hayewa zuwa Firimiya Lig a Ingila, Cheikh Tiote, ya tabbatar da rahoton cewa dan wasan ya fadi ya mutu a filin wasa yau litinin a sabuwar kulob dinsa a kasar China.

Emanuele Palladino, ya fadawa gidan telebijin na Sky Sports cewa, "ina mai bakiin cikin tabbatar da cewa Cheikh Tiote ya rasu bayan da ya fadi a filin wasan kungiyarsa sabuwa ta Beijing Enterprises."

Shi ma tsohon wakilin dan wasan, Serge Trimpont, ya fadawa kafofin yada labarai na kasar Belgium cewa da gaske ne dan wasan ya rasu.

A cikin watan Fabrairu ne Cheikh Tiote, mai shekaru 30 da haihuwa, ya koma kasar China domin bugawa kungiyar Beijing ENterprises wadda ke rukuni na biyu na wasannin Lig na kasar, a bayan da ya buga wasa daya tak ma kungiyar Newcastle United a rukunin Lig na Championship na Ingila, rukunin da kungiyar ta lashe kuma yanzu ta haye zuwa Firimiya Lig.

Cheikh Tiote ya lashe Kofin Kasashen Afirka da kasarsa ta Ivory Coast a shekarar 2015, koda yake ya samu rauni bai buga wasan karshen ba. Har ila yau ya buga ma kasar a gasar cin kofin duniya ta 2014.

An haifi Cheikh Tiote a Yamoussoukoro, daga baya kuma yana dan samari mai shekaru goma sha wani abu sai ya koma kasar Belgium a bayan da kungiyar Anderlecht ta dauki kwantarakiinsa., ya fara yi mata wasa a 2005.

A shekarar 2010, kungiyar Twente Enschede ta kasar Netherlands ta sayar da shi ma kungiyar Newcastle United ta Ingila a kan kudi fam miliyan uku da rabi. Yayi shekara 6 da rabi yana buga ma kungiyar ta Newcastle.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG