Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon kafa Na Duniya


Это футбол!!!
Это футбол!!!

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, manyan Kungiyoyin kwallon kafa na Kasar Spain Barcelona da Real Madrid na zawarcin dan wasan kwallon kafa na Manchester United, mai suna Anthony Martial.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na shirin dawo da tsohon dan wasan tsakiyanta Cesc Fabregas, Wanda ya koma kungiyar Chelsea da taka leda.

Shi kuwa Ashely Young, na Manchester united, kungiyoyi har guda hudu ne wadanda ke buga firimiya lig ke zawarcin sa, Kungiyoyin sune Everton, Westbromwich, Watford da kuma Swansea.

Real Betis na zawarcin Fabian Orellana, Juventus tasa yuro miliyan €25 domin sayen Franck Kessie dan kasar Ivory Coast, wanda kungiyoyin Arsenal da Chelsea ke zawarcinsa a karshen kakar kwallon bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

XS
SM
MD
LG