Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jahar Legas Ta Umurci Mazauna Birnin Su Toshe Ramukan Beraye


Gwamnatin jahar Legas ta ce tana yin duk yadda zata iya yi domin tabbatar da samun nasarar dakile annobar cutar zazzabi lassa kamar yadda ta sami nasara akan hana cutar Ebola yaduwa a fadin jahar.

Gwamnatin ta shawarci jama'ar jahar da su toshe duk wasu ramukan da beraye ka iya amfani dasu wajan shiga cikin gidajen su, da kuma kiyayewa daga cin nama bera, da kuma duk wani abinci da beran ya taba.

A wani taron manema labarai akan yadda za'a dakile cutar ta lassa, kwamishinan lafiya na jahar Legas Dr Jide Idris ya tabbatar da cewa acikin mutane 20 da vake zargi da kamuwa da cutar, sakamakon bincike ya tabbatar da cewa 14 daga cikin su basa dauke da cutar.

Kwamishinan ya kara da cewa yariya ta karshe da ta nuna alamun kamuwa da cutar tana da shekary 27 ne da haihuwa, kuma ta yi zirga zirga tsakanin birnin na Legas da jahar Edo daga ranar 24, ga watan Disambar shekarar 2015, da 2 ga watan janairun shekarar 2016.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG