Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rana Dubu Ta Barawo Rana ‘Daya Ta Mai Kaya


An kama wani mutum da laifin yi ma kamfanin sayar da inshorar motoci damfara, biyo bayan samunsa da yin hatsarin mota har sama da lokuta ashirin cikin shekaru biyar.

Mutumin mai suna Navid Monjazeb, yana yin wannan sana’a mai hatsarin gaske ce, domin yana sayen mota kuma ya saya mata inshore daga baya sai ya lalata motar ya kuma shirya hatsarin karya. Domin karbar kudin inshora.

Mutumin mai suna Navid Monjazeb, an dai kama shi ne a safiyar Laraba, ana kuma tuhumarsa da laifukan damfara 12, jami’ai sunce mutumin ya karbi kudi sama da dalar Amurka dubu 55 daga kamfanonin inshora, cikin shekaru biyar.

Wani jami’in kamfanin kula da damfara na kamfanin inshore Armand Glick, yace sun fara bincikar Monjezeb, ne bayan da masu binciken hatsarurruka sukace zasu iya tabbatar da cewa duk motocin da mutumin yayi hatsari dasu dama can an lalatasu.

Jami’an ‘yan sanda dai sun fara bincike kan wannan lamari bayan da kamfanin inshora ya gano irin wannan fasali na hatsari, inda alamun zargi ya shiga ciki. Har yanzu dai ba a bayyana ba ko Monjazeb yana da lauyan da zai kare shi.

XS
SM
MD
LG